12 Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama?
13 To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”
14 Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.
15 Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”
16 Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.
17 Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje.
18 In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu.