22 Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima.
23 Sai wani ya ce masa, “Ya Ubangiji, waɗanda za su sami ceto kam, kaɗan ne?” Sai ya ce musu,
24 “Ku yi famar shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba su iya ba.
25 In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’
26 Sa'an nan za ku fara cewa, ‘Ai, mun ci mun sha a gabanka, har ka koyar a kan titi-titinmu.’
27 Shi kuwa sai ya ce, ‘Ina dai gaya muku, ku kam, ban san daga inda kuke ba. Ku tafi daga wurina, dukanku ku masu aikata mugunta!’
28 Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki.