4 Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5 Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu.”
6 Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba.
7 Sai ya ce wa mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman 'ya'yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’
8 Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki.
9 In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”
10 Wata rana yana koyarwa a wata majami'a ran Asabar,