1 To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi.
2 Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”
3 Sai ya ba su wannan misali ya ce.
4 “In waninku yana da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓata, har ya same ta ba?
5 In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki.
6 In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.’