6 In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.’
7 Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”
8 “Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba?
9 In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’
10 Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”
11 Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza.
12 Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.