8 “Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba?
9 In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’
10 Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”
11 Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza.
12 Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.
13 Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a.
14 Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara.