1 Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.
2 Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”
3 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.”
4 Bilatus ya ce wa manyan firistoci da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.”
5 Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama'a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”