24 Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.”
25 Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah.
26 Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga al'ajabai!”
27 Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.”
28 Sai ya bar kome duka, ya tashi ya bi shi.
29 Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su.
30 Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”