40 Amma zama a damana, ko a haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.”
41 Da almajiran nan goma suka ji haka, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.
42 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.
43 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.
44 Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawan kowa.
45 Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
46 Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya.