23 Sai ya ɗauki ƙoƙo kuma, bayan ya yi godiya ga Allah, ya ba su, dukkansu kuwa suka shassha.
24 Sa'an nan ya ce musu, “Wannan jinina ne na tabbatar da alkawari, wanda za a bayar saboda mutane da yawa.
25 Hakika, ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranan nan da zan sha wani sabo a Mulkin Allah.”
26 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.
27 Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe ne, domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumaki kuwa su fasu.’
28 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”
29 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe, ni kam, ba zan yi ba.”