1 Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus.
2 Bilatus ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗa.”
3 Sai manyan firistoci suka yi ta kai ƙararsa a kan abubuwa da yawa.
4 Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba ka da wata amsa? Dubi yawan maganganu da suke ba da shaida a kanka!”
5 Yesu dai har yanzu bai yi wata magana ba, har Bilatus ya yi mamaki.
6 To, a lokacin idi kuwa Bilatus ya saba sakar musu kowane ɗan sarƙa guda da suka roƙa.