37 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, kana ya cika.
38 Sa'an nan labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa.
39 Sa'ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”
40 Akwai kuma waɗansu mata da suke hange daga nesa, cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu ƙarami da Yusufu, da kuma Salome,
41 su ne waɗanda suka biyo shi, sa'ad da yake ƙasar Galili, suna yi masa hidima, da kuma mata da yawa da suka rako shi Urushalima.
42 La'asar lis, da yake ranar shiri ce, wato gobe Asabar,
43 Yusufu ya zo, mutumin Arimatiya, wani ɗan majalisa mai mutunci, wanda shi ma yake sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.