1 Bayan 'yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida.
2 Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa'azin Maganar Allah.
3 Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi.
4 Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayye yake kwance a kai.