13 Ya kuwa yardar musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shiga aladun. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugungunto ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka halaka a ruwa.
14 Daga nan sai 'yan kiwon aladen suka gudu, suka ba da labari birni da ƙauye. Jama'a suka zo su ga abin da ya auku.
15 Da suka zo wurin Yesu suka ga mai aljannun nan a zaune, saye da tufa, cikin hankalinsa kuma, wato mai aljannun nan masu yawa a dā, sai suka tsorata.
16 Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka farfaɗi abin da ya gudana ga mai aljannun da kuma aladen.
17 Sai suka fara roƙon Yesu ya bar musu ƙasarsu.
18 Yana shiga jirgi ke nan, sai mai aljannun nan a dā ya roƙe shi izinin zama a gunsa.
19 Amma Yesu bai yardar masa ba, ya ce masa, “Tafi gida wurin 'yan'uwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.”