1 Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.
2 To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,
3 su ce masa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”
4 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji, da abin da kuka gani.
5 Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.