36 Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.”
37 Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.
38 Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.
39 Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne.
40 Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya.
41 Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa,
42 su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.