1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi.
2 Ya amsa musu ya ce, “In magariba ta yi, kuka ga sama ta yi ja, kukan ce, ‘Aha, gari zai yi sarari.’
3 Da safe kuma in kun ga sama ta yi ja, ta kuma gama gari, kukan ce, ‘Yau kam, za a yi hadiri.’ Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba kwa iya gane alamun zamanin nan.
4 'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu, sai dai ta Yunusa.” Sai ya bar su ya tafi.
5 Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe, sun manta ba su kawo gurasa ba.
6 Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”