11 Amma ya ce musu, “Ba duk mutum ne zai iya ɗaukar maganar nan ba, sai dai waɗanda aka yardar wa.
12 Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”
13 Sa'an nan aka kawo masa yara ƙanana domin ya ɗora musu hannu, ya yi musu addu'a, amma almajiran suka kwaɓe su.
14 Yesu kuwa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Sama na irinsu ne.”
15 Sai ya ɗora musu hannu ya yi tafiyarsa.
16 Sai ga wani ya matso wurinsa, ya ce, “Malam, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?”
17 Sai ya ce masa, “Don me kake tambayata a kan abin da yake nagari? Ai, Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami wannan rai, to, ka kiyaye umarnan nan.”