21 Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa.
22 Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.
23 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.
24 Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!
25 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.
26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.
27 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.