15 “Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),
16 to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.
17 Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.
18 Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.
19 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!
20 Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar.
21 A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.