24 Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.
25 To, na dai gaya muku tun da wuri.
26 Saboda haka in sun ce da ku, ‘Ga shi can a jeji,’ kada ku fita. In kuwa sun ce, ‘Yana can cikin lolloki,’ kada ku yarda.
27 Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.
28 Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.
29 “Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama.
30 A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.