54 To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”
55 Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.
56 Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
57 Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Attaura da shugabanni suke tare.
58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.
59 To, sai manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi.
60 Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso,