3 Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,
4 domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”
5 “In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.
6 Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.
7 “In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.
8 Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.
9 Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka,‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,A kiyaye sunanka da tsarki.