23 Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya,
24 sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini.
25 Amma da aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi.
26 Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.
27 Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.”
28 Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!”
29 Sa'an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.”