4 Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.
5 Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta.
6 Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu.
7 Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” Wato yă ta da Almasihu daga matattu.
8 Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi.
9 Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.
10 Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto.