1 To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama'arsa baya ke nan? A'a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba'isra'ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu.
2 Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama'arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra'ila, ya ce,
3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe bagadanka na hadaya. Ni kaɗai ne na ragu, suna kuwa neman raina.”
4 Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba'al ba.”
5 Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.
6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7 To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra'ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.