30 Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu,
31 haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.
32 Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.
33 Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!
34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”
35 “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa,Har da za a sāka masa?”
36 Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.