5 In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.)
6 A'a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari'a?
7 In kuwa, a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka kara ɗaukaka shi, to, don me har yanzu ake hukunta ni a kan ni mai zunubi ne?
8 In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana yanke, cewa haka muke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.
9 To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A'a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al'ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su.
10 Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,
11 Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.