12 Domin haka, 'yan'uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa.
13 In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu.
14 Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne 'ya'yan Allah.
15 Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A'a, na zaman 'ya'ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!”
16 Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne.
17 In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.
18 Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba.