6 Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama.
7 Don ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari'ar Allah, ba kuwa zai iya ba.
8 Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.
9 Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.
10 In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.
11 In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.
12 Domin haka, 'yan'uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa.