1 Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida,
2 cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.
3 Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila!
4 Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.