2 cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.
3 Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila!
4 Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.
5 Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.
6 Ba cewa Maganar Allah ta fādi ba, don ba duk zuriyar Isra'ila ne suke Isra'ilawa na gaske ba.
7 Ba kuwa duk su ne 'ya'yan Ibrahim ba, wai don suna zuriyarsa. Amma an ce, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.”
8 Wato, zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama 'ya'yan Allah ba, a'a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.