1 Ka riƙa tuna musu su yi wa mahukunta da shugabanni ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyawan aiki.
2 Kada su ci naman kowa, kada su yi husuma, sai dai su zama salihai, suna yi wa dukan mutane matuƙar tawali'u.
3 Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha'awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.
4 Amma sa'ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga 'yan adam suka bayyana,