4 Waɗannan su ne itatuwan zaitun ɗin nan guda biyu, da fitilun nan biyu da suke a tsaye a gaban Ubangijin duniya.
5 In kuwa wani yana da niyyar cutarsu, sai wuta ta huro daga bakinsu, ta lashe maƙiyansu, duk mai niyyar cutarsu kuwa, ta haka ne lalle za a kashe shi.
6 Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala'i, a duk lokacin da suke so.
7 Bayan da suka ƙare shaidarsu, sai wata dabba mai fitowa daga mahallaka tă yaƙe su, ta cinye su, ta kashe su,
8 a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma'ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.
9 Mutanen dukkan jama'a, da kabila, da harshe, da al'umma za su riƙa kallon gawawwakinsu, har kwana uku da rabi, su kuwa ƙi yarda a binne su.
10 Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a'aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.