13 Tana yin manyan abubuwan al'ajabi, har ma tana sa wuta ta zuba a ƙasa daga sama, a gaban idon mutane.
14 Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.
15 An kuma yardar mata ta busa wa siffar dabbar nan rai, har siffar dabbar nan ma ta iya yin magana, ta kuma sa a kashe waɗanda suka ƙi yi wa siffar dabbar nan sujada.
16 Har wa yau, sai ta sa a yi wa kowa alama a hannun dama, ko a goshi, manya da yara duka, mawadata da matalauta, ɗa da bawa,
17 har ba mai iya saye ko sayarwa sai ko yana da alamar nan, wato, sunan dabbar nan, ko kuwa lambar sunanta.
18 Wannan abu sai a game da hikima. Duk mai basira ya ƙididdige lambar dabbar nan, don lamba ce ta wani mutum, lambar kuwa ɗari shida ce da sittin da shida.