4 Mala'ika na uku ya juye abin da yake a tasarsa a koguna da maɓuɓɓugan ruwa, sai suka zama jini.
5 Na kuwa ji mala'ikan ruwa yana cewa,“Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka,Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.
6 Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da na annabawa,Ga shi kuwa, ka ba su jini su sha.Sakamakonsu ke nan!”
7 Sai na ji wata murya a bagadin ƙona turare, tana cewa,“Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,Hukuncinka daidai yake, na adalci ne kuma!”
8 Sai mala'ika na huɗu ya juye abin da yake a tasarsa a rana, sai aka yardar mata ta ƙona mutane da wuta.
9 Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala'i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.
10 Mala'ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,