5 A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”
6 Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu.Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.
7 Amma mala'ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan buɗa maka asirin matar nan, da kuma na dabbar nan mai kawuna bakwai, da ƙaho goma, da take ɗauke da ita.
8 Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.
9 Fahimtar wannan abu kuwa, sai a game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar take a zaune a kai.
10 Har wa yau kuma, sarakuna ne guda bakwai, waɗanda biyar daga cikinsu aka tuɓe, ɗaya yana nan, ɗayan bai zo ba tukuna, sa'ad da ya zo kuwa, lalle zamaninsa na lokaci kaɗan ne kawai.
11 Dabbar da take nan dā, a yanzu kuwa ba ta, ita ce ta takwas, daga cikin bakwai ɗin nan kuma ta fito, za ta kuwa hallaka.