20 Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama!Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”
21 Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce,“Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.
22 Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba,Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba,Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,
23 Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba,Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba,Don attajiranki, dā su ne ƙusoshin duniya,An kuma yaudari dukkan al'ummai da sihirinki.
24 Har an tarar hakkin jinin annabawa da na tsarkaka suna a wuyanta, da kuma na duk waɗanda aka kashe a duniya.”