21 Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce,“Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.
22 Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba,Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba,Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,
23 Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba,Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba,Don attajiranki, dā su ne ƙusoshin duniya,An kuma yaudari dukkan al'ummai da sihirinki.
24 Har an tarar hakkin jinin annabawa da na tsarkaka suna a wuyanta, da kuma na duk waɗanda aka kashe a duniya.”