15 Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa.
16 Birnin murabba'i ne, tsawonsa da fāɗinsa duka ɗaya ne. Sai ya auna birnin da sandarsa, mil dubu da ɗari biyar, tsawonsa, da fāɗinsa da zacinsa, duka ɗaya suke.
17 Ya kuma auna garunsa, kamu ɗari da arba'in da huɗu ne na mutum, wato, na mala'ika ke nan.
18 Garun kuwa da yasfa aka gina shi, birnin kuma da zinariya zalla, garau kamar ƙarau.
19 An kuma ƙawata harsasan garun birnin da kowane irin dutse mai daraja. Yasfa shi ne na farko, na biyu saffir, na uku agat, na huɗu zumurrudu,
20 na biyar onis, na shida yaƙutu, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha ɗaya yakinta, na sha biyu kuma ametis.
21 Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu'ulu'u ne goma sha biyun, kowace ƙofa da lu'ulu'u guda aka yi ta, hanyar birnin kuwa zinariya ce zalla garau kamar ƙarau.