1 Sa'an nan, sai ya nuna mini kogin ruwan rai, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago,
2 ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar 'ya'ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al'ummai ne.
3 Ba sauran wani abin la'antarwa, amma kursiyin Allah, shi da Ɗan Rago, zai kasance a cikinsa. Bayinsa za su bauta masa,
4 za su kuma ga fuskarsa, sunansa kuwa zai kasance a goshinsu.