6 Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.
7 Sai ya je ya ɗauki littafin nan daga hannun dama na wanda yake a zaune a kan kursiyin.
8 Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu'o'in tsarkaka.
9 Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa,“Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa,Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininkaDaga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,
10 Ka mai da su firistoci mallakar Allahnmu, za su kuwa mallaki duniya.”
11 Sa'an nan na duba, sai na ji muryar mala'iku masu yawa, a kewaye da kursiyin, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubbai,
12 suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!”