3 Ga kuma wani mala'ika ya zo ya tsaya a gaban bagadin ƙona turare, riƙe da tasar zinariya ta turaren ƙonawa. Sai aka ba shi turare mai yawa, domin ya haɗa da addu'o'in tsarkaka duka a kan bagadin ƙona turare na zinariya a gaban kursiyin.
4 Sai hayaƙin turaren ya tashi daga hannun mala'ikan tare da addu'o'in tsarkaka, ya isa a gaban Allah.
5 Sai mala'ikan ya ɗauki tasar nan ta turaren ƙonawa, ya cika ta da wuta daga bagadin ƙona turare, ya watsa a kan duniya, sai aka yi ta aradu, da ƙararraki masu tsanani, da walƙiya, da kuma rawar ƙasa.
6 Sa'an nan mala'ikun nan bakwai masu ƙaho bakwai ɗin nan, suka yi shirin busa su.
7 Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
8 Mala'ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini,
9 sulusin halittar da suke a ruwa suka mutu, sulusin jiragen ruwa kuma suka hallaka.