3 To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”
4 Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
5 Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru.
6 To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu.
7 Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.”
8 Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?”
9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan.