42 Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.”
43 Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!”
44 Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”
45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi.
46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
47 Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka?
48 In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.”