45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi.
46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
47 Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka?
48 In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.”
49 Amma ɗayansu, wai shi Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba.
50 Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk jama'a ta halaka.”
51 Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a,