11 Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”
12 Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi,
13 suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafa ne, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan.
14 Kayafa kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawara, cewa ya fiye musu mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a.
15 Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu,
16 Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wadda take jiran ƙofa, sa'an nan ya shigo da Bitrus.
17 Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A'a, ba na ciki.”