15 Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu,
16 Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wadda take jiran ƙofa, sa'an nan ya shigo da Bitrus.
17 Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A'a, ba na ciki.”
18 To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.
19 Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwa tasa.
20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.
21 Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.”