18 To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.
19 Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwa tasa.
20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.
21 Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.”
22 Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”
23 Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?”
24 Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.