24 Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.
25 To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai ya mūsu ya ce, “A'a, ba na ciki.”
26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dangin wanda Bitrus ya fille wa kunne, ya ce, “Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?”
27 Sai Bitrus ya sāke yin musu. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.
28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, wai don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa.
29 Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?”
30 Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.”